Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta lallasa gwamnan Bauchi a rumfarsa

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta lallasa gwamnan Bauchi a rumfarsa

An kaddamar da kirgan kuri'u a rumfunan zabe daban-daban a jihar Bauchi. Abin ban mamaki shine gwamnan jihar, Barista Muhammad Abubakar, na jam'iyyar All Progressives Congress APC ya sha kaye a rumfarsa ga Bala Muhammad na PDP.

Yayinda ake sanar da sakamakon zaben rumfar gwamnan dale Gindin Durumi a kwaryan Bauchi, jami'in hukumar INEC, Chinedu Onora, ya laburta cewa gwamnan ya samu jimillar kuri'u 288 yayinda Kauran Bauchi ya samu 358.

Wannan na nuni ga cewa Sanata Bala Mohammad ya lallasa gwamna mai ci har gidansa da tazarar kuri'u 70.

Mutanen da ke wajen sun nuna farin cikinsu matuka ga wannan nasara.

Shin gwamna MA zai kai labari kuwa?

Asali: Legit.ng

Online view pixel