Kiri da muzu: An ga wakilan PDP na rabawa masu zabe kudi a Abuja

Kiri da muzu: An ga wakilan PDP na rabawa masu zabe kudi a Abuja

An ga wasu wakilan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suna rabawa masu zabe kudi a rumfar zabe mai lamba 001 da ke Pilot Primary School a Bwari Central.

Al'umma sunyi cincirindo zuwa rumfar zaben wadda kuma ofishin rajista ne na INEC.

An gano wani wakilin jam'iyya rataye da tambarin PDP yana rabawa masu zabe N200 yayin da suka zagaye shi.

Ya kan fara tambayan katin zaben mutum kafin daga bisani ya mika masa kudi sannan sai mai kada kuri'an ya tafi ya zabi jam'iyyar na PDP.

Kiri da muzu: An ga wakilan PDP na rabawa masu zabe kudi a Abuja
Kiri da muzu: An ga wakilan PDP na rabawa masu zabe kudi a Abuja
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha ke gudana a Sokoto, JIgawa da Kebbi

A dayen bangaren an gano wata wakiliyar jam'iyyar PDP da ake yiwa lakabi da "Mama" inda ta ke rabawa mutane N500 kafin suyi zabe kamar yadda na mijin ya keyi.

Wani mai zabe da ya ce sunansa Bonaventure ya ce kafin wakilan na PDP su iso, wani jami'in All Progressives Congress (APC) ya yi rabon N500 kuma ya karbi nasa.

"Ai PDP sunyi kokari. Da farko 'yan APC sun zo sun rabawa mutane N500 domin a zabe jam'iyyarsu.

"Na karbi kudinsu amma duk da haka PDP na zaba. Ban san ko zaben APC dole ne ba," inji shi.

Akwai jami'an tsaro masu yawa a rumfar zaben amma babu wanda ya hana sayan kuri'un a cikinsu.

A halin yanzu ana gudanar da zaben Ciyaman da Kansila a babban birnin tarayya Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel