Masu shirin zabe sun tarwatse bayan ‘Yan bindiga sun rikita Akwa-Ibom

Masu shirin zabe sun tarwatse bayan ‘Yan bindiga sun rikita Akwa-Ibom

Dazu nan mu ka samu labari cewa an samu wasu ‘Yan bindiga da su ka sace kaf kayan zaben da ake shirin aiki da su a wani yanki a jihar Akwa-Ibom. Wannan abu dai ya faru ne dazu nan da safe.

Kamar yadda labari yake zuwa mana daga Jaridar The Cable, wasu mutanen ne su ka shigo cikin Garin Ini a Akwa-Ibom dauke da makamai, inda su ka dauke kayan zaben gwamna bayan sun rikta ko ina da harbin bindigogi.

Wadannan mutane da ba a iya gane su ba, sun dauke akwatun zabe ne da kuma takardun dangwala kuri’a da sauran kayan aiki a wasu rumfunan zabe 2 da ke cikin yankin karamar hukumar Ini da ke jihar ta Akwa-Ibom dazu.

KU KARANTA: An kai hari a wani Gari a Kaduna ana shirin zaben Gwamna

Masu shirin zabe sun tarwatse bayan ‘Yan bindiga sun rikita Akwa-Ibom
An yi awon gaba da kayan aikin zabe a wani Gari a Akwa-Ibom
Asali: Facebook

Mutanen da ke zaune a wannan yanki sun bayyana mana cewa wadannan mutane sun shigo garin ne su na buda wuta da manyan bindigogi. Wannan ne ya bada ‘yan bindigar su ka fito daga motocin su, su ka sace kayan zaben.

Tuni dai kowa ya watse ya bar tashar akwatin zabe na farko da na biyu da ke cikin Garin na Ini bayan da wadannan ‘yan bindiga su ka iso da manyan bindigogi a cikin motoci 3 ana shirin kada kuri’a domin su tsira da rayukan su.

Gwamna Udom Emmanuel dai yana neman tazarce ne a karkashin jam’yyar PDP. Sai dai gwamnan ya samu sabani da tsohon Maigidan sa watau Sanata Godswill Akpbapio na APC a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel