Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki a wasu mazabu a jihar Kogi

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki a wasu mazabu a jihar Kogi

- Wasu yan bindiga sun yadu a wasu yankunan Lokoja, babbar birnin jihar Kogi

- Maharan na ta harbe-harbe da kwace akwatunan zabe

- Mutane sun tsere daga wuraren domin tsiratar da rayuwarsu

Wasu yan banga sun yadu a wasu yankunan Lokoja, babbar birnin jihar Kogi inda suke ta harbe-harbe da kwace akwatunan zabe, kamfanin dillancin labaran ta ruwaito.

A daidai lokacin wannan rahoton, mun ci cewa wasu yan banga cikin shigar yan sanda da sojoji na bogi na tsorata masu zabe a mazabun da ke kallon Bishop Delisle Catholic Cathedral a Lokoja.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki a wasu mazabu a jihar Kogi
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki a wasu mazabu a jihar Kogi
Asali: Facebook

Wani ma’aikaci mai suna Sunday Adwjoh, ya fada ma NAN cewa wasu mutane da dama daga mazabar Karaworo sun tsere zuwa harabar cocin domin tsira.

Mista Adwjoh wanda yayi Magana akan wayar tarho yace “a yanzu haka da nake yi maku Magana, dukkaninmu mun kwankwata domin gudun kada harbi ya same mu.”

KU KARANTA KUMA: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi ke gudana a Nasarawa, Niger da Kwara

Hakazalika a mazabar Oke Egbe mazaba mai lamba 01 a yammacin Yagba a Kogi an rahoto cewa an harbi wani mutum a kafarsa lokacin da wasu mutane suka kai mamaya mazabar don sace akwatin zabe da sauran kayayyaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel