Magudin zabe: 'Yan daba sun tilastawa al'umma zaben APC a Ogbomosho

Magudin zabe: 'Yan daba sun tilastawa al'umma zaben APC a Ogbomosho

An tilastawa wasu masu zabe dangwalawa 'yan takarar jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a karamar hukumar Ogbomosho ta Kudu da ke jihar Oyo.

Wasu 'yan daba dauke da makamai ne da raba kansu rumfunan zabe mai lamba 5, 6 da 7 a gunduma ta 4 da ke Ogbomosho na Kudu inda suke tilastawa masu zabe nuna musu kuri'arsu bayan sun dangwale.

Wannan magudin zaben da 'yan daban ke aikatawa ya sanya wasu da dama sun fasa zaben inda suka rika komawa gidajensu.

Magudin zabe: 'Yan daba sun tilastawa al'umma zaben APC a Ogbomosho
Magudin zabe: 'Yan daba sun tilastawa al'umma zaben APC a Ogbomosho
Asali: Twitter

Wannan lamarin yana faruwa ne a rumfar zaben Buhari Abdulfatai, dan takarar Sanata na APC da ya lashe zabe a yankin a ranar 23 ga watan Fabrairu.

DUBA WANNAN: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha ke gudana a Sokoto, JIgawa da Kebbi

Nasarar da Abdulfatai ya samu ya bashi damar zama sanata na farko da ya lashe zabe sau biyu a mazabar Oyo ta Arewa.

A yau, 'yan Najeriya suna zaben gwamnonin su karo na shida tun bayan da Najeriya ta koma mulkin demokradiya a shekarar 1999.

A kalla mutane 37 ne ke takarar gwamna a jihar ta Oyo.

Sai dai wadanda suka fi karfi a takarar sune Oluseyi Makinde na jam'iyyar PDP da Adebayo Adelabu na jam'iyyar APC.

Jam'iyyun siyasa da dama sun goyi bayan 'yan takarar biyu daf da zaben.

Tsohon gwamnan jihar, Adebayo Alao-Akala na jam'iyyar Action Democratic Party da ake ganin jigo ne a siyasar jihar Oyo ya janye takararsa ya goyi bayan Mr Adelabu na APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel