Yanzu-yanzu: Sai na fi Buhari yawan kuri'u - Ganduje yayinda ya kada kuri'arsa

Yanzu-yanzu: Sai na fi Buhari yawan kuri'u - Ganduje yayinda ya kada kuri'arsa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa yana kyautata zaton samun kuri'u fiye da abinda shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaben shugaban kasan ranar 23 ga watan Febrairu, 2019.

Yayinda yake magana bayan kada kuri'arsa a rumfar zaben ranar Asabar, Ganduje ya bayyana cewa ko shakka babu zai lashe zabensa da tazara mai fadi.

Yace: "Na yi farin cikin yadda mutane suka fito, musamman mata. Wannan ya kara min karfin gwiwan cewa zanyi nasara a wannan zabe da babban tazara. Ina sa ran samun kuri'u fiye wanda Buhari ya samu makonni biyu da ya gabata."

Gwamnan ya yabawa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC kan yadda suka shirya kansu a wannan zabe.

Kana ya yabawa jami'an tsaro kan aikin da sukeyi don tabbatar da cewa an yi zabe cikin zaman lafiya.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Daga fara zabe, an hallaka mutane 3 a jihar Rivers

Mun kawo muku rahoton cewa an ji harbin bindigogi a wani harin fashi da aka kai a cikin Garin na Manchok.

Wasu masu fashi da makami ne su ka burma wani shagon da ake dillacin kudi da kimanin karfe 9:30 na daren jiya.

Jama’a da-dama dai sun tsere a lokacin da aka ji harbe-harben bindigogin ko ta ina a cikin gari inda kowa yake neman inda zai fake. Wannan ya sa har ma’aikatan zabe da ke aiki a yankin su ka tsere domin gudun a hallaka su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa Ko a http://twitter.com/legitnghausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel