Jama’a sun kidime bayan ‘Yan fashi sun shiga Garin Manchok

Jama’a sun kidime bayan ‘Yan fashi sun shiga Garin Manchok

Mun samu labari daga hukumar dillacin labarai cewa an ji harbe-harbe a Garin Manchok da ke cikin karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna a jiya Ranar Juma’a yayin da ake gab da zaben gwamnoni.

Jama’a sun kidime bayan ‘Yan fashi sun shiga Garin Manchok
An kai hari a wani Gari a Kaduna ana shirin zaben Gwamna
Asali: UGC

Kamar yadda labari ya zo mana, an ji harbin bindigogi a wani harin fashi da aka kai a cikin Garin na Manchok. Wasu masu fashi da makami ne su ka burma wani shagon da ake dillacin kudi da kimanin karfe 9:30 na daren jiya.

Jama’a da-dama dai sun tsere a lokacin da aka ji harbe-harben bindigogin ko ta ina a cikin gari inda kowa yake neman inda zai fake. Wannan ya sa har ma’aikatan zabe da ke aiki a yankin su ka tsere domin gudun a hallaka su.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna ya fadi inda zai koma aiki idan PDP ta karbe mulki

Wani wanda abin ya auku a gaban sa, ya bayyanawa manema labarai cewa wasu mutane 3 ne su ka shigo cikin Gari rike da bindigogi. Kamar yadda mu ka ji, Malaman zaben sun dawo bakin aiki bayan jami’an tsaro sun kawo doki.

Malam Balarabe Danjuma, wanda ke da shago a Kaueyn ya fadawa ‘yan jarida cewa ‘yan fashi sun yi gaba da wata jaka da ke dauke da kudi har Naira miliyan 5 a cikin shagon sa. Danjuma yace wannan ne karo na 2 da aka yi masa fashi.

Mukaila Danjuma wanda abin ya auku a gaban sa ya bayyana cewa abubuwa sun dawo daidai ne bayan Jami’an tsaro sun shigo garin. Garin Manchok ne dai kauyen mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Arch. Bernabas Bala Bentex.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel