Yanzu-yanzu: Daga fara zabe, an hallaka mutane 3 a jihar Rivers

Yanzu-yanzu: Daga fara zabe, an hallaka mutane 3 a jihar Rivers

Labarin da ke shigo mana yanzu na nuna cewa akalla mutane uku sun rasa rayukansu da safiyar ranar zabe a jihar RIvers, kuku maso kudancin Najeriya.

Wani matashi mai sune Micheal Abednego, ya gamu da ajalinsa ne a hannun wani jami'in dan sanda a karamar hukumar Ahaoda ta yamma dake jihar.

Hakazalika, wata jigor jam'iyyar APC da a'a gano sunanta ba har yanzu da wani matashi suna rasa rayukansu a karamar hukumar Ndoni, Ogba/Egbema.

Mun kawo muku rahoton cewa wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan bangan siyasa sun kai wa jami'an hukumar zabe INEC hari a safiyar yau a karamar hukumar Ezza ta Arewa da ke jihar Ebonyi.

Lamarin ya faru ne a makarantar sakandire na Umuoghara da ke Okposi misalin karfe 2:15 na dare.

Matasan sun tsere da wasu muhimman kayayakin zabe na INEC sannan suka bankawa ofishin hukumar zaben wuta.

Hukumar ta INEC tana amfani da makarantar na a matsayin ofishin rajista.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, ASP Loveth Odah ta tabbatar da afkuwar lamarin a yayin da ake tuntube ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel