Zabe: Jami'an EFCC sun kama jakunkuna makil da kudi a Makurdi (Hotuna)

Zabe: Jami'an EFCC sun kama jakunkuna makil da kudi a Makurdi (Hotuna)

An kama dan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Benue, Emmanuel Jime dauke da buhunna makil da kudi a ranar zabe.

Jami'an hukumar EFCC ne suka damke Mr Jime inda suke zarginsa da sayan kuri'u.

An kama shi ne a rumfar zabe na North Bank da ke Makurdi, babban birnin jihar.

'Yan bangan siyasa ne jam'iyyar APC sun yi kaiwa jami'an EFCC hari a yunkurin su na hana a kama Mr Jime.

Jami'an na EFCC sun kwace dumin kudaden da aka same shi da su a cikin buhunna.

Hukumar ta EFCC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an ta kama makuden kudade a cikin buhunna a Makurdi amma ba ta ambaci sunan Mr Jime ba.

Zabe: Jami'an EFCC sun kama jakunkuna makil da kudi a Makurdi (Hotuna)
Kudade da jami'an EFCC suka kama a garin Makurdi na jihar Benue
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha ke gudana a Sokoto, JIgawa da Kebbi

Zabe: Jami'an EFCC sun kama jakunkuna makil da kudi a Makurdi (Hotuna)
Jakunkuna makil da sabbin kudade da ake zargin za ayi amfani da shi ne wurin sayan kuri'a
Asali: Twitter

Zabe: Jami'an EFCC sun kama jakunkuna makil da kudi a Makurdi (Hotuna)
Motar jami'an EFCC da wasu bata gari suka kaiwa farmaki yayin da jami'an EFCC suka kama kudi a Makurdi
Asali: Twitter

Zabe: Jami'an EFCC sun kama jakunkuna makil da kudi a Makurdi (Hotuna)
Sabbin kudade cikin jaka da jami'an EFCC suka kama a garin Makurdi na jihar Benue
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel