Yan daba sun cinna wa makarantar firamare dauke da kayan zabe wuta a jihar Benue

Yan daba sun cinna wa makarantar firamare dauke da kayan zabe wuta a jihar Benue

Yan daba sun kona kayayyakin zabe na yankin Mbalom da ke karamar hukumar Gwer East a safiyar ranar Asabar,9 ga watan Maris.

A cewar idanun shaida, yan daban sun iso wajen ne sai suka kama harbi a sama kafin su cinna wa makarantar firamare na RCM Aya wuta dauke da kayayyakin zaben.

Ngunan Yongo, jami’ar zabe na karamar hukumar, ta tabbatar da afkuwar lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a wayar tarho.

Yan daba sun cinna wa makarantar firamare dauke da kayan zabe wuta a jihar Benue
Yan daba sun cinna wa makarantar firamare dauke da kayan zabe wuta a jihar Benue
Asali: Twitter

Tace ba a riga an rarraba kayayyakin zabe ga mazabun da ke yankin ba a lokacin da aka kai harin.

Sai dai kuma babu jami’in hukumar na da wucin gadi da suka ji rauni.

Ta yi bayanin cewa daga baya za a yanke hukunci akan gudanarwar zaben.

KU KARANTA KUMA: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi ke gudana a Nasarawa, Niger da Kwara

Thaddeus Uja, wani babban jami’in hukumar ma ya tabbatar da harin.

Mista Ujah yace an tura shi yankin ne kwanan nan don haka ba zai iya has ashen adadin ma’aikatan wucin gadi da aka rasa ba har sai ya duba takarda.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan bangan siyasa sun kai wa jami'an hukumar zabe INEC hari a safiyar yau a karamar hukumar Ezza ta Arewa da ke jihar Ebonyi.

Lamarin ya faru ne a makarantar sakandire na Umuoghara da ke Okposi misalin karfe 2:15 na dare.

Matasan sun tsere da wasu muhimman kayayakin zabe na INEC sannan suka bankawa ofishin hukumar zaben wuta. Hukumar ta INEC tana amfani da makarantar na a matsayin ofishin rajista.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel