Yanzu-yanzu: 'Yan bangar siyasa sun bankawa ofishin INEC wuta a Ebonyi

Yanzu-yanzu: 'Yan bangar siyasa sun bankawa ofishin INEC wuta a Ebonyi

Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan bangan siyasa sun kai wa jami'an hukumar zabe INEC hari a safiyar yau a karamar hukumar Ezza ta Arewa da ke jihar Ebonyi.

Lamarin ya faru ne a makarantar sakandire na Umuoghara da ke Okposi misalin karfe 2:15 na dare.

Matasan sun tsere da wasu muhimman kayayakin zabe na INEC sannan suka bankawa ofishin hukumar zaben wuta.

Hukumar ta INEC tana amfani da makarantar na a matsayin ofishin rajista.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, ASP Loveth Odah ta tabbatar da afkuwar lamarin a yayin da ake tuntube ta.

Duk da haka dai an fara gudanar da zabe a wasu yankuna na jihar a babban birnin jihar, Abakalilki.

Ga hotunan yadda matasan suka kone ofishin na INEC.

Yanzu-yanzu: 'Yan bangar siyasa sun bankawa ofishin INEC wuta a Ebonyi
Yanzu-yanzu: 'Yan bangar siyasa sun bankawa ofishin INEC wuta a Ebonyi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matakan tsaro 12 da ya kamata ku kiyaye a zaben gobe Asabar

Yanzu-yanzu: 'Yan bangar siyasa sun bankawa ofishin INEC wuta a Ebonyi
Yanzu-yanzu: 'Yan bangar siyasa sun bankawa ofishin INEC wuta a Ebonyi
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel