Zabe: An kama wata mota makare da kudi a jihar Sokoto

Zabe: An kama wata mota makare da kudi a jihar Sokoto

- An kama wata mota dankare da kudade a jihar Sokoto daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnoni da nayan majalisun jihohi a fadin kasar

- Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa tare da jami'an tsaro ne suka kama mota kirar Jeep

- An kama motar mai lamba ABC 924 LU a kan titin Garba Duba da ke Sokoto a daren Juma'a

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an kama wata mota dankare da kudade a jihar Sokoto daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnoni da nayan majalisun jihohi a fadin kasar.

An tattaro cewa hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa tare da jami'an tsaro ne suka kama mota kirar Jeep makare da kudi da ake zargin za a yi amfani da su ne wajen sayen kuri'u a jihar.

Zabe: An kama wata mota makare da kudi a jihar Sokoto
Zabe: An kama wata mota makare da kudi a jihar Sokoto
Asali: Twitter

An kama motar mai lamba ABC 924 LU a kan titin Garba Duba da ke Sokoto a daren Juma'a, 8 ga watan Maris da misalin karfe 10:30 inda aka kai motar hedikwatar 'yan sanda a jihar.

Daga nan ne aka fito da buhunhunan kudi domin yin bincike. An yi ta kokarin jin ta bakin kakakin 'yan nda kan lamarin, yayin da jami'an tsaron suka hana daukar hotunan kudin.

KU KARANTA KUMA: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi ke gudana a Nasarawa, Niger da Kwara

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta cika hanu da akawun gwamnatin jihar Kwara, Sulaiman Ishola, kan laifin zare makudan kudi biliyan daya da rabi domin sayen kuri'u ranar zabe.

Majiya daga hukumar EFCC ta laburtawa manema labaran Cable da yammacin Juma'a. Wannan babban kamu da EFCC tayi ya biyo bayan damke akawun gwamnatin jihar Im, Uzoho Casmir, wanda ya saci biliyan daya bisa umurnin mai gidansa gwamnan jihar, Rochas Okorocha.

Hukumar tace an yi niyyar amfani da kudin ne wajen sayen kuri'u jama'a a zaben gwamnoni da yan majalisun dokoki da zai gudana ranar Asabar, 9 ga watan Maris, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel