Zaben gwamnoni: Jahohin Arewa da jam'iyyar PDP za ta iya lashewa

Zaben gwamnoni: Jahohin Arewa da jam'iyyar PDP za ta iya lashewa

Yayin da sakamakon zabukan gwamnoni da kuma 'yan majalisun tarayya a dukkanin fadin tarayyar Najeriya, ya zuwa yanzu zabukan sun soma daukar wani sabon salo.

A yankin Arewa dai muna da jahohi 19 ne kuma za'a yi zabukan gwamnoni da na 'yan majalisu a dukkan jahohin banda jihar Kogi inda za'a yi zaben 'yan majalisu kawai.

Zaben gwamnoni: Jahohin Arewa da jam'iyyar PDP za ta iya lashewa
Zaben gwamnoni: Jahohin Arewa da jam'iyyar PDP za ta iya lashewa
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta tattaro maku hasashen masu sharhi kan al'amurran siyasa jahohin da ake tunanin jam'iyyar PDP zata iya lashewa, kuma ga su kamar haka:

Kano: Jihar Kano dai ana ganin Kwankwaso na da dumbin masoya kuma hakan zai iya baiwa jam'iyyar PDP nasara akan gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Sokoto: Ita ma wannan jihar ana ganin kasantuwar gwamnan jihar na yanzu, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ke neman tazarce kuma yana da magoya baya musamman ma duba da irin kuri'un da jam'iyyar sa ta samu ta PDP a zaben Shugaban kasa, ana ganin zai iya lashe zaben.

Adamawa: Saboda Atiku Abubakar dan jihar ne kuma jam'yyar PDP ce ta lashe zaben shugaban kasa a jihar, ana ganin APC zata iya faduwa.

Taraba: Kasantuwar jihar daman can ta PDP ce da wata jam'iyya bata taba ci ba, haka kuma gwamnan jihar a yanzu dan PDP ne ana ganin kamar da wuya ace APC ta lashe zaben jihar.

Benuwe: Jihar Benue dai yanzu haka PDP ce ke mulkar ta kuma musamman ma saboda sakamakon da APC ta samu a zaben shugaban kasa a jihar, ana ganin cewa jam'iyyar PDP ce zata lashe zaben jihar.

Filato: Ita ma jihar Filato yanzu haka hukumar zabe ta bayyana zaben ne a matsayin wanda bai kammalu ba kuma ta ce zata sake zaben a wasu mazabu. Kafin aukuwar hakan, jam'iyyar APC da PDP suna kan-kan-kan ne da juna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel