Da dumin sa: Hukumar EFCC na tuhumar wani gwamnan APC da badakalar Naira biliyan 1

Da dumin sa: Hukumar EFCC na tuhumar wani gwamnan APC da badakalar Naira biliyan 1

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta cafke babban akawun gwamnatin jihar Imo, mai suna Uzo Casmir bisa zargin karkatar da kudin jihar.

Haka ma dai hukumar ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) tana zargin babban akawun da hade kai da gwamnan jihar ta Imo, Mista Rochas Okorocha wajen karkatar da kudin jahar da yakai Naira biliyan 1 da dubu hamsin don sayen kuri'u a zaben gwamna da 'yan majalisun jihar da za'a gudanar a ranar Asabar.

Da dumin sa: Hukumar EFCC na tuhumar wani gwamnan APC da badakalar Naira biliyan 1
Da dumin sa: Hukumar EFCC na tuhumar wani gwamnan APC da badakalar Naira biliyan 1
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: INEC zata sake zabukan 'yan majalisun tarayya a jihar 14

Kamar yadda muka samu, hukumar ta EFCC shiyyar jihar Enugu ce ta tabbatar da kamen babban jami'in gwamnatin jihar inda suka ce kuma yanzu haka suna kan bincike kan lamarin.

A wani labarin sashin dake kula da manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Yaba, jihar Legas ya fara gudanar da bincike bisa zargin cin hanci da ake yiwa DPO mai kula da sashin Pen Cinema mai suma Harrison Nwabuisi.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa, DPO tare da wandasu jami’an ‘yan sanda ana zargin sune da amsar na goro daga wajen mazauna unguwar Alimi Ogunyemi dake Ijeiye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel