Dankari: Ana saura sa'o'i 24 zabe, sakataren PDP, shugabanninta 12 sun fita daga jam'iyyar

Dankari: Ana saura sa'o'i 24 zabe, sakataren PDP, shugabanninta 12 sun fita daga jam'iyyar

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party ( PDP), a jihar Borno ta y babban rashi ana saura awa 24 zaben gwamnan jihar da yan majalisun dokoki inda sakataren jam'iyyar, shugabanninta na kananan hukumomi 12 suka koma jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Wasu manyan da suka sauya sheka tare da sakatare, Baba Ahmed Mustapha, sune shugabannin matasan PDP da shugabannin matan jam'iyyar.

Yayinda yake jawabi ga yan jarida a sakatariyan APC dake Maiduguri, sakataren yace ya fita daga PDP ne saboda rashin da'a da adalci da ya fitini jam'iyyar.

Mustapha ya ce tun ranar Alhamis, 7 ga watan Maris ya fita daga jam'iyyar kuma a fahimtarsa, cigaba da zama a ciki uk da rashin adalcin da ke faruwa tamkar zalunci ne ga mabiyansa.

Yace: "Na sauya sheka zuwa APC ne saboda rashin adalci da yaudara dake PDP a Borno. Ana saura sa'o'i 24 zabe amma babu wanda ya sanda zaman PDP, babu yakin neman zabe ana gab da zabe."

"PDP na da dan takara amma ya yi shiru tsit baya yakin neman zabe, wannan na nuni ga cewa yaudarar mutane yakeyi"

"Illan sauya shekana zai bayyana gobe inda aka yi zabe. Ina kira ga mambobin PDP su zo su hada kai da APC domin cigaban jihar Borno".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel