Yanzu-yanzu: Saraki ya shigesu, EFCC ta damke akawun jihar Kwara kan amfani da N1.5bn wajen sayan kuri'u

Yanzu-yanzu: Saraki ya shigesu, EFCC ta damke akawun jihar Kwara kan amfani da N1.5bn wajen sayan kuri'u

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta cika hanu da akawun gwamnatin jihar Kwara, Sulaiman Ishola, kan laifin zare makudan kudi biliyan daya da rabi domin sayen kuri'u ranar zabe.

Majiya daga hukumar EFCC ta laburtawa manema labaran Cable da yammacin Juma'a.

Wannan babban kamu da EFCC tayi ya biyo bayan damke akawun gwamnatin jihar Im, Uzoho Casmir, wanda ya saci biliyan daya bisa umurnin mai gidansa gwamnan jihar, Rochas Okorocha.

Hukumar tace an yi niyyar amfani da kudin ne wajen sayen kuri'u jama'a a zaben gwamnoni da yan majalisun dokoki da zai gudana ranar Asabar, 9 ga watan Maris, 2019.

Ku kasance tare da mu domin cikakken rahoton..

Asali: Legit.ng

Online view pixel