Matakan tsaro 12 da ya kamata ku kiyaye a zaben gobe Asabar

Matakan tsaro 12 da ya kamata ku kiyaye a zaben gobe Asabar

Akwai 'yan Najeriya da dama suke fargabar zuwa rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben gwamnoni da 'yan majalisar jiha da za a gudanar a jihohi 29 na kasar nan a gobe Asabar saboda matsalolin tsaro da aka fuskanta a wasu sassan Najeriya yayin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Hakan ya sanya mutane a wasu yankuna musamman kudancin kasar nan sun ki fitowa wurin zabe domin kada kuri'unsu.

Ga wadanda ke damuwa a kan tsaron lafiyarsu a gobe, mu kawo muku wasu hanyoyi kaucewa fadawa cikin rikici a wurin zaben a gobe.

Matakan tsaro 12 da ya kamata ku kiyaye a zaben gobe Asabar
Matakan tsaro 12 da ya kamata ku kiyaye a zaben gobe Asabar
Asali: Facebook

1. Ka tabbatar ka tafi wurin zabe da katin zabe na ainihi domin kaucewa samun matsalar da jami'an INEC ko jami'an tsaro

2. Mutum ya kauracewa saka kayan masu tallata dan takarar domin kada abokan hammaya su kai masa farmaki

3. Mutum ya isa rumfar zabe da wuri domin ya kada kuru'insa

4. Kada ka fada wa kowa dan takarar da za ka zaba a rumfar zaben

5. Guji yin musu ko gardama a kan 'yan takara ko kushe wani dan takara

6. Ka mika wayar tarho din ka ga jami'in zabe kafin shiga rumfar kada kuri'a

DUBA WANNAN: Wamakko ya yi karin haske a kan zargin tarbarbarewar dangantakarsa da Sultan

7. Ka tabbatar ba bu wanda ya ga dan takarar da ka zaba a lokacin da ka ke dangwale kuri'ar ka

8. Ka kasance mai halin dattaku yayin da ka ke rumfar zaben

9. Ka koma gefe inda hukumar zabe ta ce a tsaya ga wadanda ke son su tsaya har sai an kammala kidiya kuri'un

10. Kada kayi kasa a gwiwa wurin sanar da jami'an tsaro idan ka ga wani mutum da baka amince da shi ba

11. Ka guji aikata magudin zabe kamar sace akwatin zabe ko aringozon kuri'u da zai iya jefa rayuwarka cikin hatsari

12. Ka bar rumfar zaben da zarar ka lura hankalin ka bai kwanta ba ko kaga alamar tarzoma za ta tashi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel