Akwa Ibom: Sai anyi zabe duk da kone ofishin mu da aka yi - INEC

Akwa Ibom: Sai anyi zabe duk da kone ofishin mu da aka yi - INEC

Kwashinan zabe na jihar Akwa Ibom, Mike Igini ya ce za a gudanar da zabe a karamar hukumar Asutan na jihar duk da cewa gobara ta lashe ofishin hukumar zabe mai zaman kanta INEC na jihar.

A yayin da ya ke tsokaci a kan gobarar da ta faru a yau, kwamishinan ya ce za a gudanar da zaben na ranar Asabar saboda muhimman kayayakin zaben da za ayi amfani da su ba su kone ba.

Ya amsa cewar wasu na'urorin tantance katin zabe, da injin janareta da komfutoci da wasu kayayakin aiki sun kone sakamakon gobarar amma kididigar da suka gudanar a karamar hukumar ya nuna cewa za a iya gudanar da zabe.

"Babu ja da baya a kan zaben ranar 9 ga watan Maris. Za a gudanar da zabe kamar yadda aka tsara duk da makircin da wasu suka kula," inji shi.

DUBA WANNAN: Rundunar Soji ta yiwa manya ofisoshi canje-canjen wurin aiki (jerin sunaye)

Ga hotunan yadda gobarar tayi barna a ofishin hukumar na INEC a kasa:

Kone ofishin INEC na Akwa Ibom ba zai hana zabe ba - INEC
Yadda gobara tayi barna a ofishin INEC na karamar hukumar Ibesipko na jihar Akwa Ibom
Asali: Twitter

Kone ofishin INEC na Akwa Ibom ba zai hana zabe ba - INEC
Wasu daga cikin kayayakin da suka kone a ofishin INEC na karamar hukumar Ibesipko na jihar Akwa Ibom
Asali: Twitter

Kone ofishin INEC na Akwa Ibom ba zai hana zabe ba - INEC
Yadda gobara tayi barna a ofishin INEC da ke jihar Akwa Ibom
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel