An daga zaben majalisa a jihar Adamawa sakamakon rasuwan dan takarar APC

An daga zaben majalisa a jihar Adamawa sakamakon rasuwan dan takarar APC

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta dage zaben majalisar dokokin jiha na mazabar Nasarawa/Binyeri a jihar Adamawa.

Kwamishanan INEC na jihar, Kashim Gaidam, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris inda ya yi bayanin cewa dage zaben ya zama wajibi ne bisa ga mutuwan wani dan majalisa wanda shine dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Mun kawo muku rahoton cewa dan takaran APC, Adamu Kwanate, ya rasu ne ranar Laraba, 6 ga watan Maris, 2019 inda ya yanke jiki ya fadi yayin yakin neman zabe kuma ya cika a wata asibiti dake Yola.

Gaidam ya ce dage zaben zai baiwa jam'iyyar APC da jama'arsa daman maye gurbinsa da wani dan takara.

Yace: "Mun samu wasikar jam'iyyar da majalisar dokokin kan rasuwar dan takaran kuma mun maida musu da amsan cewa zamu basu mako daya su maye gurbinsa."

Za muyi bayani ga hedkwata idan aka canza sunan domin sanya sabuwar ranan zaben."

A bangare guda, an tura jami'an yan sanda garin Jalingo, babbar birnin jihar Taraba doin kwantar da kuran rikicin kabilancin da ta faru a Jeka da Fari, kusa da gidan gwamnatin jihar.

Tashin hankalin ya fara ne yayinda aka dabawa wani matashi wuka. Kawai sai yan uwan wanda aka raunata suka kai mumunan hari kan kabilar Hausa/Fulani dake unguwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel