Da dumin sa: Hukumar INEC za ta sake zaben 'yan majalisar tarayya a jahohi 14 gobe

Da dumin sa: Hukumar INEC za ta sake zaben 'yan majalisar tarayya a jahohi 14 gobe

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa a tarayyar Najeriya watau Independent National Electoral Commission (INEC) tace yanzu ta yanke shawarar ta sake gudanar da zabukan kujerun wasu 'yan majalsun tarayya a jahohi 14 a fadin kasar.

Kamar dai yadda muka samu daga hukumar, zabukan sun shafi na kujerun majalisaun dattawa guda bakwai da kuma na 'yan majalisun wakilai 24 a jahohin 14.

Da dumin sa: Hukumar INEC za ta sake zaben 'yan majalisar tarayya a jahohi 14 gobe
Da dumin sa: Hukumar INEC za ta sake zaben 'yan majalisar tarayya a jahohi 14 gobe
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari zai sayar da madatsan ruwan Najeriya 6

Legit.ng Hausa ta samu cewa shugaban hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC), farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana wannan matsayar ta hukumar a garin Abuja yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan zabukan watau Inter-Agency Consultative Committee on Elections Security (ICCES).

A cewar sa, hukumar ta dauki matakin soke zabukan wasu rumfuna ne a yankunan lokacin zabukan da suka gabata sati biyu da ya wuce sakamakon hargitsi, satar akwati da kuma wasu sauran laifuffukan da suka jibinci zaben.

A wani labarin kuma, sashin dake kula da manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Yaba, jihar Legas ya fara gudanar da bincike bisa zargin cin hanci da ake yiwa DPO mai kula da sashin Pen Cinema mai suma Harrison Nwabuisi.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa, DPO tare da wandasu jami’an ‘yan sanda ana zargin sune da amsar na goro daga wajen mazauna unguwar Alimi Ogunyemi dake Ijeiye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel