Yanzu-Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kamo dan takarar gwamnan wata jiha na APC

Yanzu-Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kamo dan takarar gwamnan wata jiha na APC

Wata kotun majistare ta jihar Ribas da ke zaman ta a garin Fatakwal, babban birnin jihar ta bayar da takardar izinin kamo dan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), mai suna Mista Nsima Ekere.

Babban alkalin kotun dai ne S.D. Andrew-Jaja tare da da taimakawar mai shari'a Katungo Moljengo ne suka bayar da umurnin a wani hukuncin da suka yanke da suka ce yayi dai dai da Sashe na 138 na kundin laifuka na 2015.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kamo dan takarar gwamnan wata jiha na APC
Yanzu-Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kamo dan takarar gwamnan wata jiha na APC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Atiku ya aike da sako ga masoyasan sa

Legit.ng Hausa ta samu cewa hukuncin kotun dai ya biyo bayan shari'ar koken da wani mutum ya shigar a gaban alkalan mai lamba PMC/MISC/15/2019 kan wasu zarge-zargen aikata ba dai dai ba ta anfani da wani kamfani mai suna Multi-Intelligence Development Limited.

A wani labarin kuma, Sashin dake kula da manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Yaba, jihar Legas ya fara gudanar da bincike bisa zargin cin hanci da ake yiwa DPO mai kula da sashin Pen Cinema mai suma Harrison Nwabuisi.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa, DPO tare da wandasu jami’an ‘yan sanda ana zargin sune da amsar na goro daga wajen mazauna unguwar Alimi Ogunyemi dake Ijeiye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel