Rashin amincewa da shan kayi: Wani babban Sanatan APC ya yi amai ya lashe

Rashin amincewa da shan kayi: Wani babban Sanatan APC ya yi amai ya lashe

Wani babban Sanatan jam’iyyar APC kuma jigo a majalisar dattawan Najeriya, tsohon gwamnan jahar Akwa Ibom Sanata Godswill Akpabio ya sanar da janye karar daya shigar gaban kotu inda yake kalubalantar kayin daya sha a zaben Sanatoci daya gudana makonni biyu da suka gabata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Lauyan Sanata Akpabio, Sunday Ameh ne ya sanar da haka a yayin zaman babbar kotun tarayya dake Abuja na ranar Juma’a, sai dai bai bayyana dalilin janyewar ba.

KU KARANTA: Kaico! Malamin Islamiyya ya murde wuyan dalibinsa a jahar Taraba

Sanata Akpabio ya sha kayi ne a kokarinsa na yin tazarce a kujerar Sanatan daya hau tun a zaben shekarar 2015, dan takarar jam’iyyar PDP, Chris Ekpeyong ne ya samu nasarar damfarashi da kasa da kuri’u 118,215, yayin da Akpabio keda 83,158.

Sai dai wani na hannun daman Akpabio, Wole Arisekola ya bayyana cewa Akpabio ya dauki matakin janye karar ne don baiwa dukkanin bangarorin biyu daman warware sabaninsu a kotun turaibuna da kotun daukaka kara ta kafa don sauraron koke koken zabe.

Sai dai duk janyewar da yayi, Alkalin kotun, Valentine Ashi ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, da kada ta kuskura ta mika ma dan takarar jam’iyyar PDP Chris Ekepeyong shaidar lashe zabe.

Sai dai a hannu guda, lauyan hukumar INEC, Tanimu Inuwa ya bayyana ma menam labaru cewa babbar kotun tarayya bata da hurumin sauraron karar daya shafi zabe, don haka yace sai dai su hadu a kotun sauraron koke koken zabe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel