Kada ka kashe kanka - Hukumar fansho ta roki malamin makaranta dan shekara 65 a Bauchi

Kada ka kashe kanka - Hukumar fansho ta roki malamin makaranta dan shekara 65 a Bauchi

Hukumar fansho (PenCOM) a ranar Juma’a, 8 ga watan Maris ta sha alwashin taimakawa wani malamin makaranta mai ritaya dan shekaru 65 mai suna Mista Alhamdu Dan’azumi wajen samun kudin sallamarsa.

Shugaban bincike da dabaru na hukumar, Dr Aminu Farouk ya bayyana alkawarin ne yayinda yake mayar da martani akan barazanar kashe kansa da Dan’Azumi yayi a wani hira da yayi da kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar 6 ga watan Maris a Legas.

An rahoto cewa shiga lamarin da yan jarida suka yi ne ya ceci rayuwar Dan’azumi.

Kada ka kashe kanka - Hukumar fansho ta roki malamin makaranta dan shekara 65 a Bauchi
Kada ka kashe kanka - Hukumar fansho ta roki malamin makaranta dan shekara 65 a Bauchi
Asali: Depositphotos

Rahoton na nuni ga cewa Dan Azumi yayi tafi harabar cibiyar kungiyar yan jaridar Najeriya wato Nigerian Union of Journalist (NUJ), Bauchi, inda yayi yunkurin kashe kanshi akan rashin biyan shi kudin sallama bayan yayi ritaya daga aiki.

An rahoto Dan’Azumi na fadin “nayi aiki har na tsawon shekaru 35 kuma nayi ritaya kuma ina da yancin karban kudin sallama.”

An kara da cewa Dan’ Azumi yayi ikirarin cewa yana da bashi har na naira 800,000 sannan kuma yana dauke da cutar kanjamau tun shekaru 20 da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Zukata sun cika da tsoro a Rivers yayinda sojoji suka mamaye fadar sarki Ateke Tom

Farouk ya nuna bakin ciki akan wannan lamari, sannan ya roki Dan’azumi da ya rubuta wasikar korafi zuwa ga hukumar PenCom, kamar yanda hukumar za ta dauki mataki cikin gaggawa.

Farouk yace PenCom za ta cigaba da aiwatar da ayyuka don amfanar da yan Najeriya da suka tsufa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel