Rundunar soji tace ba za ta sassautawa masu ta da rikici ba a zaben gwamnoni da na majalisan jihohi

Rundunar soji tace ba za ta sassautawa masu ta da rikici ba a zaben gwamnoni da na majalisan jihohi

Shugaban hafsan sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya ce rahotannin sirri da aka samu sun nuna cewa ‘yan siyasa na yunkurin tayar da zaune tsaye domin lalata zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun Jihohi da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro da manyan jami’ai da Kwamandojin rundunar ta kasa.

Buratai ya yi nuni ga afkuwar wasu tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar a yayinda aka gudanar da zaben shugaban kasa, inda ya ce, jami’an na shi ba za su saurarawa duk wani dan siyasa da ya yi yunkurin tsalma baki a kan yanda zaben ke gudana ba.

Rundunar soji tace ba za ta sassautawa masu ta da rikici ba a zaben gwamnoni da na majalisan jihohi
Rundunar soji tace ba za ta sassautawa masu ta da rikici ba a zaben gwamnoni da na majalisan jihohi
Asali: UGC

Wasun su ma suna da shirin yin shigan burtu a cikin wakilan abokanan hamayyan su, su aiwatar da kisan kai, su yi amfani da kafafen yada labarai na yanar gizo domin yin batunci da yada labaran karya domin lalata aiwatar da zaben cikin lumana. Ba za mu taba amincewa su cimma manufar na su ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sake samun girgizan kasa a Abuja

A watan Fabrairu, Shugaba Buhari ya bayar da umurni ga hukumomin tsaro da kar su sassautawa duk wanda ya kwaci akwatin zabe. a sa’ilin da abokanan hamayya suka yi suka a kan hakan, rundunar Sojin cewa suka yi za su tabbatar da bin umurnin na shugaban kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel