Rundunar Soji ta yiwa manya ofisoshi canje-canjen wurin aiki (jerin sunaye)

Rundunar Soji ta yiwa manya ofisoshi canje-canjen wurin aiki (jerin sunaye)

A jiya Hukumar sojojin Najeriya ta fitar da sunayen wasu jami'an ta da aka yiwa canji wurin aiki da kuma sabbin nade-nade na manyan sojoji.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Kakakin hukumar soji, Kwanel Sagir Musa ta ce wandanda canjin ya shafa ya hada da Manjo Janar ECN Obi da aka tura Hedkwatan Tsaro a matsayin Shugaban Tsaro da sanya ido a kan ayyuka.

Manjo Janar LF Abdullahi da aka dauke daga hedkwatan Ilimi na Soji aka mayar da shi shugaba a hedkwatan tsaro sashin harkokin tsaffin sojoji.

Rundunar Soji ta yiwa manya ofisoshi canje-canjen wurin aiki (jerin sunaye)
Rundunar Soji ta yiwa manya ofisoshi canje-canjen wurin aiki (jerin sunaye)
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Tsaro: An fitar da kididdigar adadin mutanen da aka kashe a Zamfara cikin mako guda

Manjo Janar OG Adeniyi da aka dako daga hedkwatan tsaro na soji aka nada shi mataimakin kwamandan Operation Lafiya Dole da ke Arewa maso Gabas.

Brig Janar GK Nwosu shi kuma an nada shi shugaban riko na makarantar horas da sojoji na musamman yayin da aka dako Brig Janar CA Apere daga makarantar horas da sojoji na musamman zuwa 82 Division a matsayin shugaban soji.

An nada Brig Janar KI Yusuf a matsayin Kwamanda na makarantar nazarin kudi na Soji yayin da Brig Janar MNB Mamman daga hedkwatan Injiniyoyin Sojin Najeriya (Sappers Engineering Nigeria Ltd) ya koma direktan ayyuka na Soji.

Kazalika, Janar AD Gbadebo daga hedkwatan Injiniyoyin Soji ya koma mataimakin shugaba a makarantar injiniyoyin soji sannan Janar SS Araoye na makarantar tsare-tsare na Sojoji ya zama kwamanda a cibiyar ayyuka na sojoji.

Janar CA Thomas daga makarantar Sojoji na jihar Legas ya zaa mai bayar da shawara a kan harkokin Jinsi a hedkwatan tsaro.

Saura da canjin ya shafa sun hada da Kwanel DC Bako na Operation Lafiya Dole da aka nada shugaban riko, Kwanel SO Omotosho kuma an mayar da shi sashin injiniyoyi na lantarki da Injina zai kasance shigaba na riko sai kuma Kwanel LG Lepdung zai cigaba da kasancewa a hedkwatan sojoji a matsayin shugaban riko na sashin bincike da cigaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel