Bulus: Gwamnati ta kwace kundin Patience Jonathan $8.4m bisa ga umurnin kotu

Bulus: Gwamnati ta kwace kundin Patience Jonathan $8.4m bisa ga umurnin kotu

Kotuna kolin Najeriya ta tabbatar da shari'ar da babban kotun tarayya da ke zauna a Legas ta zantar na kwace kudi mallakan uwargidar tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, Patience Jonathan, dala milyan takwas a dubu dari hudu.

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gano wasu makudan kudi a asusunan banki daban-daban da Patience Jonathan ta boye kudin ba ba zata iya bayanin yadda ta samesu ba.

A shari'ar da gangamin alkalai kotun koli biyar suka yanke ranar Juma'a, 8 ga watan Maris, an yi watsi da daukaka karar da Patience Jonathan tayi na hana gwamnatin tarayya kwace kudin.

Kotun ta umurci Jonathan ta bayyana gaban babban kotun tarayya kuma tayi bayanin yadda ta samu kudaden, hakan ne kawai zai hana gwamnati kwace kudin.

A baya mun kawo muku rahoton cewa wata kotu dake zaman ta a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ta bayar da umurni ga jami'an gwamnatin kasar na su karbe tare da killace wasu gidajen uwar gidan tsohon shugaban kasar Najeriya Dame Patience Jonathan, bisa zargin da ake yi mata na mallakar su ta hanyar da bata dace ba.

Kamar dai yadda muka samu, daya daga cikin alkalin kotun mai suna Nanmdi Dimgba ne ya bayar da wannan umurnin na karbe gidajen biyu daga hannun uwargidan tsohon shugaban kasar na wucin gadi, domin hukumar EFCC ta samu damar kammala gudanar da binciken ta a kan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel