Zukata sun cika da tsoro a Rivers yayinda sojoji suka mamaye fadar sarki Ateke Tom

Zukata sun cika da tsoro a Rivers yayinda sojoji suka mamaye fadar sarki Ateke Tom

Tsoro ya cika zukatan mutane a jihar Rivers a jiya bayan sojoji cikin motoci sama da 20 sun kai mamaya sannan suka yi kawanya a fadar Amanyanabo na masarautar Okochiri, karamar hukumar Okorika da ke jihar Rivers, mai martaba Ateke Tom.

Majiyoyin garin sun bayyana cewa an kasha mutum daya, amma ba’a tabbatar da hakan ba a daren jiya yayinda aka kama mutane biyar a lokacin mamayar, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Mai martaba Ateke Tom, tsohon Shugaban masu fafutuka a Niger Delta ya kasance daya daga cikin sarakunan da ke goyon bayan tazarcen Gwamna Nyemsom Wike.

Zukata sun cika da tsoro a Rivers yayinda sojoji suka mamaye fadar sarki Ateke Tom
Zukata sun cika da tsoro a Rivers yayinda sojoji suka mamaye fadar sarki Ateke Tom
Asali: Facebook

Sai dai majiyaru ta Vanguard bata tabbatar ba ko suna binciken makamaki da yan daba ne, amma wata majiyar sojoji tace “rundunar sun yi aiki ne bisa ga tsegumin da suka samu.”

An tattaro cewa an samu tsahin hankali a masarautar, yayinda sojojin suka ziyarci fadar sannan suka tafi da bakin sarkin guda biyar.

KU KARANTA KUMA: Rundunan Soji za ta tura jirginta Kwara domin sanya ido a zabe

An kuma raoto cewa a lokacin aikin sojojin sun kashe karnuka uku mallakar sarkin sannan suka lalata kamaran tsaro da ke fadar.

Da yake tabbatar da lamarin, Tamuno Peters, daya daga cikin hadiman sarkin ya bayyana cewa sojojin sun harbi mutum guda yayin mamayar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel