Wamakko ya yi karin haske a kan zargin tarbarbarewar dangantakarsa da Sultan

Wamakko ya yi karin haske a kan zargin tarbarbarewar dangantakarsa da Sultan

A jiya ne Sanata Aliyu Wamakko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto ya ce kyakyawar alakar da ke tsakanin sa da Sarkin Musulmi, Muhammadu sa'ad Abubakar III tana nan yadda ta ke.

"Akwai kyakyawar alaka tsakani na da Sultan da ma masarautar musulunci na jihar Sokoto baki daya," inji shi.

Wamakko ya yi wannan maganar ne a wurin wani addu'a na musamman da aka shirya domin rokon Allah ya sanya a gudanar da zaben gwamna da 'yan majalisun jihar cikin zaman lafiya da lumana, inda ya ce, "Sultan baya fifita ko wane dan siyasa, shi uba ne ga kowa."

Akwai kyakyawar danganta tsakani na da Sultan - Wamakko
Akwai kyakyawar danganta tsakani na da Sultan - Wamakko
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsohon mataimakin gwamnan PDP a Katsina ya fita daga jam'iyyar

Ya ce Sarkin Musulmi yana da daraja da kima a idon kowa kuma al'umma na kaunarsa.

Ya ce jam'iyyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta cigaba da girmama sarakunan gargajiya saboda irin darajar da suke da shi.

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa wasu mutane sanya da kayan sojoji sunyi kutse fadar sarkin Ochiri, Ateke Tom da ke karamar hukumar Okrika na jihar Rivers.

Kafin zamansa sarki, Ateke ya kasance shugaba na matasa da ke tayar da kayan baya a yakin Neja Delta amma daga bisani shi da yaransa suka rungumi shirin afuwa da gwamnatin tarayya ta yiwa tsageran Neja Delta a shekarar 2008.

Wata majiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar sumamen da aka kai yana da alaka da zaben gwamna da 'yan majalisun jiha za a gudanar a gobe Asabar.

A bangarenta, rundunar 'yan sandan Najeriya ta aike da 'yan sanda 15,544 zuwa jihar Rivers domin tabbatar da tsaro yayin gudanar da zaben.

KU KARANTA: Gwamna Bagudu ya yi rashin shakikinsa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel