Rundunan Soji za ta tura jirginta Kwara domin sanya ido a zabe

Rundunan Soji za ta tura jirginta Kwara domin sanya ido a zabe

Rundunan so ji zata tura jirginta zuwa jihar Kwara don sanya ido a zaben gwamna da na yan majalisar jiha da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

A cewar Kayode Egbetokun, kwamishinan rundunan yan sandan jihar Kwara, an yanke shawaran ne don tabbatar da cikakkiyar aiki.

Ya bukaci al’umma da kada su ji tsoro, su fito su halarci zabe.

Ya ce: “Za a tura jirgin sama don kula da harkan zabe, a maimakon jirgin yan sanda da aka yi amfani da shi a zaben baya. Amman kada al’umman suji tsoro idan suka ga jirgin, saboda tabbatar da tsaro. Su fito kwansu da kwarkwatan su don kada kuri’an su."

Rundunan Soji za ta tura jirginta Kwara domin sanya ido a zabe
Rundunan Soji za ta tura jirginta Kwara domin sanya ido a zabe
Asali: Twitter

A cewar Air Commodor A. Adamu, shugaban rundunan sojin sama reshen jihar Kwara, za a yi amfani da jirgin rundunan soji ne saboda jirgin da aka yi amfani da shi a baya yana daga cikin jirage da aka tura yankin Arewa maso Gabas don yakar yan ta’adda.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan iska sun cinna ma ofishin INEC wuta a Akwa Ibom

A cewar shi, amfani da jirgi ya fi “sauri, sauki kuma zai taimaka cikin gaggawa” a wuraren da ke fuskantan kalubale."

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel