Tsohon hadimin gwamnan Kwara da wasu da dama sun sauya sheka zuwa APC

Tsohon hadimin gwamnan Kwara da wasu da dama sun sauya sheka zuwa APC

Alhaji Aliyu Mohammed-Salihu, wani tsohon hadimin Gwamna AbdulFatah Ahmed na Kwara akan harkokin sarauta ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All progressives Congress (APC) tare da wasu dubban mambobin PDP.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa masu sauya shekar sun fito ne daga yankuna uku a Gwanara da ke karamar hukumar Barren da ke jihar.

Mohammed-Salihu wanda a kwanaki yayi murabus daga matsayinsa na adimin gwaman, ya sanar da sauya shekarsu yayin zantawa da manema labarai a Ilorin a ranar Juma’a, 8 ga watan Maris.

Tsohon hadimin gwamnan Kwara da wasu da dama sun sauya sheka zuwa APC
Tsohon hadimin gwamnan Kwara da wasu da dama sun sauya sheka zuwa APC
Asali: Depositphotos

Yace akwai bukatar sauya shekarsu duba ga tarin nasarorin da APC ta samu a dukkanin matakai na ci gaba.

Ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin tabbatar da nasarar dan takarar gwamna da yan majalisa na APC a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan iska sun cinna ma ofishin INEC wuta a Akwa Ibom

Da yake tarban masu sauya shekar, Shugaban APC a yankin Gwanara, Alhaji Umar Kutosi, yayi godiya ga sabbin mambobn akan hukuncinsu na dawowa jam’iyyar.

Ya basu tabbacin cewa dukkanin mambobin jam’iyyar za su samu kula iri guda a shirye-shiryen abubuwa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel