Mutane 7 sun mutu, gidaje 50 sun kone a Kogi sanadiyar rikicin kabilanci

Mutane 7 sun mutu, gidaje 50 sun kone a Kogi sanadiyar rikicin kabilanci

- Rahotanni sun kawo cewa rikicin kabilanci ya barke a jihar Kogi

- Lamarin yayi sanadiyar mutuwar mutane bakwai da kuma kona gidaje 50

- Rikicin ya barke ne a tsakanin Egbura Mozum da Bassa Kwomu a yankin

Akalla mutane bakwai sun mutu sannan aka kona akalla gidaje 50 sanadiyar rikici da ya barke tsakanin kauyukan Sheria da Oguma a karamar hukumar Bassa dake a jihar Kogi a safiyar jiya.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa rikicin ya kasance tsakanin Egbura Mozum da Bassa Kwomu a yankin.

Wassu da ake zargin cewa yan ta’adda ne sun kai hari kauyukan Sheria da Oguma a karamar hukumar wanda yayi sanadiyan mutuwan wassu tare da asaran kaddarori; yayin da wassu suka tsere daga gidajen su.

Mutane 7 sun mutu, gidaje 50 sun kone a Kogi sanadiyar rikicin kabilanci
Mutane 7 sun mutu, gidaje 50 sun kone a Kogi sanadiyar rikicin kabilanci
Asali: UGC

Kakakin rundunar yan sanda, William Aya, wanda ya tabbatar da lamarin, yace rundunan ta gano gawar mutum daya.

Yace shugaban rundunan mai jagorancin Bassa ya samu kira cewa an kai hari a yankin inda cikin gaggawa ya tura mutanensa don tabbatar da kwanciyar hankali.

KU KARANTA KUMA: NANS da wasu kungiyoyi 6 sun marawa dan takarar gwamna na APC baya a Nasarawa

Yace an mika wa babban asibitin yankin gawar don gudanar da gwaje gwaje.

Aya ya bayyana cewa kwamishinan yan sanda a jihar, Hakeem Busari, ya tura runduna zuwa kauyukan dake cikin tashin hankali. Yace lamarin yayi sauki a kauyukan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel