Yanzu Yanzu: Yan iska sun cinna ma ofishin INEC wuta a Akwa Ibom

Yanzu Yanzu: Yan iska sun cinna ma ofishin INEC wuta a Akwa Ibom

- Wasu yan iska ne sun kona wani ofishin hukumar zabe mai zaman kantaa karamar hukumar Ibesikpo Asuntan da ke jihar Akwa Ibom

- Hakan yayi sanadiyar lalacewar wasu kayayyakin zabe, inda yan sanda suka yi nasarar kare wasu daga cikin kayayyakin

- Babu bayani kan ko hakan zai shafi zaben da za a gudanar a gobe a yankin

Wasu da ake zargin yan iska ne sun kona wani ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a karamar hukumar Ibesikpo Asuntan da ke jihar Akwa Ibom.

Lamarin da ya afku ana gobe zaben gwamnoni da na majalisar jihohi yayi sanadiyar lalacewar wasu kayayyakin zabe.

Wani idon shaida ya fada ma jaridar The Cable cewa yan sanda sun yi nasarar kare wasu kayayyakin zabe.

Yanzu Yanzu: Yan iska sun cinna ma ofishin INEC wuta a Akwa Ibom
Yanzu Yanzu: Yan iska sun cinna ma ofishin INEC wuta a Akwa Ibom
Asali: Twitter

Akwa Ibom na daga cikin jihohin da aka samu yawan rikice-rikice a lokacin zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokokin kasa.

Mike Igini, kwamishinan zabe na jihar, ya ziyarci inda abun ya afku. Sai dai babu wani bayani da ke nuni ga ko lamarin zai shafi zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris a yankin.

KU KARANTA KUMA:Majalissun tarayya: Buhari da shugabannin APC za su yanke shawaran yankunan da za su rike manyan mukamai

A wani lamari na daban, Legit.ng ta raoto cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar matar Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina. Jaridar Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a daren jiya, Alhamis, 7 ga watan Maris.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel