NANS da wasu kungiyoyi 6 sun marawa dan takarar gwamna na APC baya a Nasarawa

NANS da wasu kungiyoyi 6 sun marawa dan takarar gwamna na APC baya a Nasarawa

Gamayyar kungiyoyin siyasa shida, harda kungiyar daliban Najeriya sun mara wa takarar Abdullahi Sule, na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) baya a jihar Nasarawa.

Malam Umar Yusuf, babban sakararen kungiyar NANS, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris a wani jawabi a madadin sauran kungiyoyin, yace kungiyoyin bakwai sun amince da za su yi aiki tare da APC a zaben gwamna da na yan majalisan jiha a ranar 9 ga watan Maris.

Yusuf yace kungiyoyin sun tsayar da Sule bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar, inda suka amince da yin aiki tare da dan takaran gwamnan.

NANS da wasu kungiyoyi 6 sun marawa dan takarar gwamna na APC baya a Nasarawa
NANS da wasu kungiyoyi 6 sun marawa dan takarar gwamna na APC baya a Nasarawa
Asali: UGC

Sunayen kungiyoyin sun hada da: Nasarawa Youths and Students Leaders Forum (NYSLF) Nasarawa Youths Empowerment Forum (NYEF) Vote in Silas Agara (VISA) – Nasarawa State deputy governor’s support group da kuma APC Comrades Forum.

Yace sauran kungiyoyin sun hada da: Indigenous Youth Forum (NIYOF) da kuma Active Females Coalition (AFC).

A cewar Lawal, kungiyoyin sun yanke shawaran tsayar da jam’iyyar APC bayan tattaunawa da aka yi a Akwanga, jihar Nassarawa, saboda tsabar goyon baya da suka samu daga Agara a baya, mataimakin gwamna kuma jigo a jam’iyyar.

A cewar shi, Gwamna Umar Al-makura ya cika alkawran yakin neman zabe na tura yara makarantu, gina makarantu a manyan cibiyoyi; hade da gine-ginen dakunan karatu.

Lawal yace kada kuri’a ga dan takaran APC zai tabbatar da inganta ayyukan alkhairi da Al-makura yayi a jihar.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyun siyasa 23 sun hade sun mara wa dan takarar PDP baya a wata jihar Arewa

Ya bayyana farin cikin shi cewa Sule ya sha alwashin yin fiye da abunda gwamnan yayi.

A cewar shi, kwarewar dan takaran a kamfani masu zaman kansu fiye da shekaru 30 zai taimaka kwarai da gaske wajen amfanar tattalin arzikin jihar.

Yace Sule ya kasance dan takara guda da ya bayyana kwarewarsa na amfanar da al’umma ba tare da nuna banbanci a yare ko a addini ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel