Majalissun tarayya: Buhari da shugabannin APC za su yanke shawaran yankunan da za su rike manyan mukamai

Majalissun tarayya: Buhari da shugabannin APC za su yanke shawaran yankunan da za su rike manyan mukamai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za su gana bayan zaben gwamnoni don yanke shawara akan tsarin rabe raben mukaman majalisa ga yankuna, a cewar wata majiya a jiya.

Shugaban kasa Buhari har ila yau, ya bayyana manufofinsa cewa wannan karon ba zai zura ido yana kallon yanda abubuwa ke gudana ba tare da ya tabuka komai ba.

Yace zai kasance cikin duk wani tattaunawa da rikice-rikice akan zaben manyan mukamai a majalissun kasar.

Jam’iyyar APC tace ita ma za ta taka rawarta a wajen zabin sabbin shugabannin majalisa.

A sakamakon zaben yan majalisan kasa da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana, APC ta lashe kujeru 65 daga cikin mazabai 109, kimanin kashi 59.6%.

Majalissun tarayya: Buhari da shugabannin APC za su yanke shawaran yankunan da za su rike manyan mukamai
Majalissun tarayya: Buhari da shugabannin APC za su yanke shawaran yankunan da za su rike manyan mukamai
Asali: Facebook

PDP ta lashe kujeru 42 kimanin kashi 40.3% sannan Young Progressives Party ta samu kashi 1%.

A majalisan wakilai kuma, APC ta lashe fiye da kujeru 230 daga cikin kujeru 360, PDP ta lashe kujeru 100.

A halin yanzu sanatoci da yan majalisan wakilai sun soma shirin neman manyan mukamai. Masu neman manyan ofisoshi a majalisan dattawa sun hada da sabbin sanatoci daga Arewa maso Gabas, Arewa ta tsakiya da Kudu maso Yamma.

Wassu daga cikin masu neman kujeran shugaban majalisan dattawa sun hada da sanata mai jagora Ahmed Lawan; tsohon sanata mai jagora Ali Ndume; tsohon Gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje, shugaban kungiyar Parliamentary Support Group (PSG) Chairman Kuma tsohon Gwamna Abdullahi Adamu da sanata Ovie Omo-Agege.

Wassu daga cikin jerin sanatoci bakwai daga Kudu maso Yamma sun soma hararar kujerar mataimakin kakakin majalisan dattawa, ko jagoran sanatoci ko mataimakin jagora.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar matar Gwamna Masari

Kakakin majalisan wakila na iya zuwa daga Kudu maso Yamma, da tsohon jagoran yan wakilai masu rinjaya, Hon Femi Gbajabiamila, a matsayin babban dan takara. Zai sake karawa da kakakin majalisa Yakubu Dogara na jam’iyyar PDP.

Wassu shugabannin jam’iyya suna bukatan a sake tantance tsarin baiwa yankuna mukamai tunda shugaban kasar ya sha alwashin kawo hadin kai a gwamnati.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel