Yanzu Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar matar Gwamna Masari

Yanzu Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar matar Gwamna Masari

- Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar matar Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina

- Lamarin ya afku ne a daren jiya, Alhamis, 7 ga watan Maris

- Masu garkuwan sun kai farmaki gidan dattijuwar surukar gwamnan da ke Katsina akan Babura sannan suka tafi da ita

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar matar Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a daren jiya, Alhamis, 7 ga watan Maris.

Yanzu Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar matar Gwamna Masari
Yanzu Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar matar Gwamna Masari
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa yan bindigan sun kai farmaki gidan dattijuwar surukar gwamnan da ke Katsina akan Babura sannan suka tafi da ita.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta sanar da cewar ta kama mutane 10 da su ka aikata laifuka daban-daban yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Katsina, Sanusi Buba, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Alhamis, yayin sanar da shirin da rundunar ‘yan sanda ta yi domin tunkarar zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki da za a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Zukata sun cika da tsoro a Rivers yayinda sojoji suka mamaye fadar sarki Ateke Tom

A cewar sa, laifukan wadanda aka kama sun hada da kokarin hana gudanar da zabe da kuma saba ka’idojin zabe. Ragowar laifukan sun hada da yin taro ba bisa ka’ida ba, damun jama’a, da amfani da mugggan makamai domin firgita ma su kada kuri’a a lokacin zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel