Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakokin kasar saboda zaben gwamnoni da na majalisar jihohi

Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakokin kasar saboda zaben gwamnoni da na majalisar jihohi

- Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakokin kasar saboda zaben gwamnoni da na majalisar jihohi

- Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau ya bayar da umurninn

- Za a rufe iyakokin ne daga yau Juma'a zuwa ranar Lahadi, 10 ga watan Maris

Ministan harkokin cikin gida, Laftanal Janar Abdulrahman Dambazau me ritaya ya yi umurnin rufe dukkanin iyakokin kasar domin zaben gwamnoni da na yan majalisar jihohi da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakokin kasar saboda zaben gwamnoni da na majalisar jihohi
Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakokin kasar saboda zaben gwamnoni da na majalisar jihohi
Asali: Facebook

Za a aiwatar da hakan ne daga ranar Juma’a, 8 ga watan Maris zuwa ranar Lahadi, 10 ga watan Maris da rana.

“Ana umurtan jama’a das u lura sannan su bayar da hadin kai," inji Babandede.

KU KARANTA KUMA: Mutane 2 sun mutu, an lalata motoci 35, an kuma fasa shaguna da dama a lokacin da bangarorin APC suka kara a Lagas

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa jam’iyyun siyasa 23 sun hade a jihar Katsina inda suka nuna goyon bayansu ga takarar Sanata Yakubu Lado na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Da yake magana a madadinsu, Shugaban jam’iyyar Progressive Peoples Alliance (PPA), Habibu Yau, yace sun yanke shawarar mara masa baya ne saboda ci gaban jiharsu.

Ya ce suna sanya ran mambobinsu su fito kwansu da kwarkwatarsu sannan su mara wa PDP baya cewa “a dukkanin kananan hukumomi 34 muna da mambobi sannan muna umartansu da su yi abunda ya kamata."

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel