Zabe: Rundunar 'yan sanda za ta aike da dubun dubatan jami'ai jihar Ribas

Zabe: Rundunar 'yan sanda za ta aike da dubun dubatan jami'ai jihar Ribas

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Rivers ta ce ta tanadi jami'a 15,544 da za su taimaka wurin samar da tsaro a zaben gwamna da 'yan majalisun jihar da za ayi a ranar Asabar mai zuwa.

Wannan na zuwa ne a lokacin da jam'iyyar PDP a jihar ke kira da Hukumar Sojin Najeriya ta saki kwamishinan Ilimi na jihar, Dr Tamunosisi Gogo-Jaja da iyalansa da kuma jagoran Arise Nigeria, Hon. Benjamim Diri da aka kama a ranar Laraba a Fatakwal.

A jawabin da ya yiwa manema labarai a ranar Alhamis a garin Fatakwal, kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Balel ya ce a kalla jami'ai 1,500 daga sauran hukumomin tsaro aka tanada domin zaben da za a gudanar a jihar.

DUBA WANNAN: Dan takarar APC da ya fadi zaben kujerar majalisar wakilai ya koma PDP

Zabe: Rundunar 'yan sanda za ta aike da jami'ai 15,544 zuwa jihar Rivers
Zabe: Rundunar 'yan sanda za ta aike da jami'ai 15,544 zuwa jihar Rivers
Asali: Twitter

Ya ce za a takaita zirga-zirgan al'umma masu shige da fice a jihar daga karfe 12 na daren Juma'a zuwa karfe 6 na yammacin ranar Asabar.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce za a rufe dukkan hanyoyin shigowa jihar har zuwa bayan zabe.

A bangarensu, shugabanin jam'iyyar PDP na jihar Rivers sun ce sojojin Najeriya sunyi awon gaba da kwamishinan ilimi na jihar, GogoJaja tare da iyalansa a lokacin da su kayi kutse cikin gidan da ke GRA Phase 3 a Fatakwal a yammacin ranar Laraba.

A sakon da jam'iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun hadimin shugaban jam'iyyar na jihar, Jerry Needam, jam'iyyar ta ce abin takaici ne yadda sojoji a Rivers suka karbe aikin 'yan sanda baya da haka sun tsunduma kansu a cikin siyasa inda wasu makiyar demokradiya ke amfani da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel