Jam’iyyun siyasa 23 sun hade sun mara wa dan takarar PDP baya a wata jihar Arewa

Jam’iyyun siyasa 23 sun hade sun mara wa dan takarar PDP baya a wata jihar Arewa

Jam’iyyun siyasa 23 sun hade a jihar Katsina inda suka nuna goyon bayansu ga takarar Sanata Yakubu Lado na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Da yake magana a madadinsu, Shugaban jam’iyyar Progressive Peoples Alliance (PPA), Habibu Yau, yace sun yanke shawarar mara masa baya ne saboda ci gaban jiharsu.

Ya ce suna sanya ran mambobinsu su fito kwansu da kwarkwatarsu sannan su mara wa PDP baya cewa “a dukkanin kananan hukumomi 34 muna da mambobi sannan muna umartansu da su yi abunda ya kamata."

Jam’iyyun siyasa 23 sun hade sun mara wa dan takarar PDP baya a wata jihar Arewa
Jam’iyyun siyasa 23 sun hade sun mara wa dan takarar PDP baya a wata jihar Arewa
Asali: UGC

A cewarsa, “a matsayin PPA na jam’iyyar siyasa da ta samar da gwamna a jihohin Abia da Imo za mu iya kai labara amma dai bisa ga fahimtarmu mun yanke shawarar kasancewa da PDP."

Ya kara da cewa: “abunda muke so kawai shine zabe cikin lumana kuma sai mun yi nasara.

KU KARANTA KUMA: Mutane 2 sun mutu, an lalata motoci 35, an kuma fasa shaguna da dama a lokacin da bangarorin APC suka kara a Lagas

“Da ace kudi muke so, dam un kasancee a gidan gwamnati amma ra’ayinmu don talaka ne sannan mun gane cewa PDP jam’iyya ce da ked a ra’ayin mutane a zuciya.”

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a yammacin ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Daura gabannin zaben gwamna da na majalisar jiha wanda za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Shugaban kasar ya isa Daura a cikin jirgin Shugaban kasa mai saukar ungulu da misalin karfe 6:50 na yamma tare da rakiyar hadimansa da iyalansa makusantansa. Ya samu tarba daga sarkin Daura, Alhaji Farouk, mataimakansa da kuma daruruwan masoyansa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel