Mutane 2 sun mutu, an lalata motoci 35, an kuma fasa shaguna da dama a lokacin da bangarorin APC suka kara a Lagas

Mutane 2 sun mutu, an lalata motoci 35, an kuma fasa shaguna da dama a lokacin da bangarorin APC suka kara a Lagas

Alamu sun nuna cewa zaben gwamnoni da yan majalisa da za a gudanar a ranar Asabar a jihar Legas na iya fuskantar tashin hankali yayin da bangarorin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar suke shiga rikici da fadace-fadace tsakanin su a yammacin ranar Alhamis.

Akalla mutane biyu ne suka mutu sannan aka lalata motoci 35 hade da fashe fashen shaguna da dama a yayin fada tsakanin bangarorin APC a Oto-Awori dake yankin Ijanikin a Legas.

Rikicin ya kasance tsakanin magoya bayan dan takaran APC daga bangaren Ojo wanda ke neman kujeran majalisa a jihar Legas da wani mamba mai nuna bakin ciki akan rashin lashe zaben fidda gwani da bai samu nasara ba a shekarar da ya gabata.

Mutane 2 sun mutu, an lalata motoci 35, an kuma fasa shaguna da dama a lokacin da bangarorin APC suka kara a Lagas
Mutane 2 sun mutu, an lalata motoci 35, an kuma fasa shaguna da dama a lokacin da bangarorin APC suka kara a Lagas
Asali: Depositphotos

An gano cewa rikicin ya barke ne a lokacinda dan takaran APC mai suna Jafo ya ziyarci fadar Oloto of Awori.

An gano cewa wassu matasa masu biyayya ga mamban jam’iyyar, mai suna Bibire, sun yi kokarin hana dan takarar shiga fadar bisa dalilin rashin lashe tikitin jam’iyyar wanda Jafo ne ya kasance sanadin hakan.

A wani lamari na daban, mun ji cewa har ya zuwa lokacinnan da zaben gwamnoni ya rage saura kwana daya tal yan siyasa basu daina sauya sheka tsakanin jam’iyyu mabanbanta, tare da kulla sabbin alaka irin ta siyasa don bukatar kashin kai ba, kamar yadda muka gani a jahar Ekiti.

Legit.ng ta ruwaito wasu jigogin jam’iyyar PDP, kuma tsofaffin yan majalisun tarayya daga jahar Ekiti, Sanata Bode Ola da Segun Ola sun jefar da kwallon mangwaro domin su huta da kuda, inda suka tattara inasu inasu suka fice daga PDP, suka yi kuma rungumi tafiyar APC.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel