Shugaba Buhari ya isa Daura gabannin zaben gwamna

Shugaba Buhari ya isa Daura gabannin zaben gwamna

A yammacin ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Daura gabannin zaben gwamna da na majalisar jiha wanda za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Shugaban kasar ya isa Daura a cikin jirgin Shugaban kasa mai saukar ungulu da misalin karfe 6:50 na yamma tare da rakiyar hadimansa da iyalansa makusantansa.

Ya samu tarba daga sarkin Daura, Alhaji Farouk, mataimakansa da kuma daruruwan masoyansa.

Shugaba Buhari ya isa Daura gabannin zaben gwamna
Shugaba Buhari ya isa Daura gabannin zaben gwamna
Asali: Twitter

An tattaro cewa uwargidan Shugaban kasar, Hajiya Aisha Buhari za ta shirya wata liyafar cin abincin dare ga kungiyoyin mata da matasa a Daura.

A wani lamari na daban, mun ji cewa mataimakin shugaban kasa Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya gudanar da yakin neman zabe Kudancin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Wasu jiga jigan PDP a jahar Ekiti sun yi wankan tsarki sun tsunduma APC

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin da ake gab da gudanar da zaben gwamnoni a fadin kasar nan, a jiya Alhamis mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya gudanar da taron yakin neman zabe a jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa, Farfesa Osinbajo tare da dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC, Prince Dapo Abiodun, sun karade kananan hukumomi na cikin birnin Ogun da suka hadar da; Ake, Isale, Gbein, Ibara, Itoku da kuma Lafenuwa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel