Kaico! Malamin Islamiyya ya murde wuyan dalibinsa a jahar Taraba

Kaico! Malamin Islamiyya ya murde wuyan dalibinsa a jahar Taraba

Wani karamin yaro mai shekaru 9 a rayuwa kuma dalibi a makarantar Muhawashat dake cikin garin Jalingo na jahar Taraba ya gamu da ajalinsa a hannun Malaminsa mai suna Hashiru Bala, bayan ya murde wuyansa har lahira.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dalibin mai suna Mohammed Sudais da ne ga wani hamshakin dan kasuwa dake zaune a garin Jalingo, kuma tun a ranar Lahadin data gabata ne aka fara nemansa ba’a ganshi ba, daidai lokacin da ya fita sallar Magariba.

KU KARANTA: Yan shi’an Najeriya sun nuna ma kasar Amurka yatsa game da kisan kiyashi da aka musu a Zaria

Kaico! Malamin Islamiyya ya murde wuyan dalibinsa a jahar Taraba
Sudais
Asali: UGC

Sai dai rashin jin duriyar Sudais ko dawowarsa daga Masallaci tasa iyayensa suka bazama nemansa, inda a sakamakon haka wani abokinsa ya bayyana ma iyayen Sudais yadda Malam Hashiru yake ta tambayarsu game da Sudais a kwanakin baya.

Daga nan ne aka gayyaci Malamin domin a ji dalilin da yasa yake tambayar Sudais, watakila a dace ya san inda yake, amma kiri da muzu ya musanta hakan, indsa yace bai ga Sudais ba, har sai da jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS suka tafi dashi.

Bayan jami’an na DSS sun tafi dashi ne sai ya tabbatar musu da cewa shi ya kashe Sudai, kuma wuyansa ya murde, da haka ya aika da shi zuwa barzahu, daga nan kuma ya jagoranci jami’an DSS zuwa wani gida daya binne gawar Sudais din.

A wani labarin kuma, wani matashi dan shekara 18, mai suna Salisu Muhammad ya fada komar Yansanda bayan an kamashi da laifin kisan mai horas da kungiyar da yake taka leda a cikinta a unguwar Yakasai ta jahar Kano, Mujittafah Musa.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar, 2 ga watan Maris da misalin karfe 11:21 na dare yayin da musun kwallo ta hadasu, inda daga nan Salisu ya dauki wuka ya daba ma Mujittafa wuka a kirjinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel