Yansanda sun kama miyagu 24 a Kaduna, sun kwace bindigu 8 daga wajensu

Yansanda sun kama miyagu 24 a Kaduna, sun kwace bindigu 8 daga wajensu

Rundunar Yansandan jahar Kaduna ta sanar da kama wasu gagga gaggan miyagun mutane su ashirin da hudu a jahar Kaduna, tare da kwace bindigu gudsa takwas da kuma alburusai da dama, kamar yadda kwamishinan Yansandan jahar ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishina Ahmad Abdurrahman ne ya tabbatar da haka a ranar Alhamis, yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin Yansandan dake garin Kaduna, inda yace sun samu wannan nasara ce bayyan kaddamar da samame na musamman akan miyagu a Kaduna.

KU KARANTA: Yan shi’an Najeriya sun nuna ma kasar Amurka yatsa game da kisan kiyashi da aka musu a Zaria

Daga cikin wadanda aka kama akwai wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifin satar mutane tare da yin garkuwa dasu, ya kara da cewa an kama sauran ne da aikata laifin fashi da makami, satar mota, sayen kayan sata, sata, dabanci, mallakan makamai ba bisa ka’ida ba da sauransu.

Haka zalika kwamishinan yace sun kwace kananan bindigu guda uku, bindigar toka daya, da wasu bindigogu guda hudu, sai kuma alburusai da dama. Bugu da kari Yansanda sun kwace motoci kirar Toyota guda 5, kwamfuta 10, allon Galaxy, wayar Samsung, atamfa, agogo, adda da sherbebiyar wuka.

Sauran abubuwan da rundunar Yansandan jahar Kaduna ta kwace daga hannun miyagun sun hada da kayan sawa na Sojoji da na Yansanda, bakaken yadi guda biyu, da kuma na’urar kallon fayafayan CD.

Daga karshe Kwamishinan yace wadanda aka kama sun bayar da muhimman bayanai game da laifukansu ga jami’an Yansanda masu gudanar da bincike, kuma da zarar sun kammala binciken zasu gurfanar dasu gaban kotu don ta hukuntasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel