Cikin Hotuna: Osinbajo ya gudanar taron yakin neman zabe a jihar Ogun

Cikin Hotuna: Osinbajo ya gudanar taron yakin neman zabe a jihar Ogun

A yayin da ranar Asabar, 9 ga watan Maris za a gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun na jiha, mun samu a jiya Alhamis, mataimakin shugaban kasa Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya gudanar da yakin neman zabe Kudancin Najeriya.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin da ake gab da gudanar da zaben gwamnoni a fadin kasar nan, a jiya Alhamis mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya gudanar da taron yakin neman zabe a jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa, Farfesa Osinbajo tare da dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC, Prince Dapo Abiodun, sun karade kananan hukumomi na cikin birnin Ogun da suka hadar da; Ake, Isale, Gbein, Ibara, Itoku da kuma Lafenuwa.

Yayin gudanar da taron yakin neman zabe, Osinbajo ya yi kira ga magoya baya da su fito kwansu da kwarkwata wajen zaben jam'iyyar APC a ranar Asabar domin ci gaba da sharbar romo na dimokuradiyya.

Osinbajo yayin girgiza magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Ogun
Osinbajo yayin girgiza magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Ogun
Asali: Twitter

KARANTA KUMA: Yansanda sun kama miyagu 24 a Kaduna, sun kwace bindigu 8 daga wajensu

Osinbajo tare da Prince Abiodun
Osinbajo tare da Prince Abiodun
Asali: Twitter

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel