Wasu jiga jigan PDP a jahar Ekiti sun yi wankan tsarki sun tsunduma APC

Wasu jiga jigan PDP a jahar Ekiti sun yi wankan tsarki sun tsunduma APC

Har ya zuwa lokacinnan da zaben gwamnoni ya rage saura kwana daya tal yan siyasa basu daina sauya sheka tsakanin jam’iyyu mabanbanta, tare da kulla sabbin alaka irin ta siyasa don bukatar kashin kai ba, kamar yadda muka gani a jahar Ekiti.

Legit.ng ta ruwaito wasu jigogin jam’iyyar PDP, kuma tsofaffin yan majalisun tarayya daga jahar Ekiti, Sanata Bode Ola da Segun Ola sun jefar da kwallon mangwaro domin su huta da kuda, inda suka tattara inasu inasu suka fice daga PDP, suka yi kuma rungumi tafiyar APC.

KU KARANTA: Dangote ne kan gaba a tsakanin attajirai mafi arziki a cikin bakaken fata

Su dai wadannan yan siyasa sun kasance yan gida daya, uwa daya uba daya ne, kuma mataimakin gwamnan jahar Ekiti, Bisi Egebeyemi ne ya jagoranci shuwagabannin jam’iyyar APC reshen jahar Ekiti wajen yin maraba da zuwansu APC.

An shirya gangamin karbar yan uwan biyu ne a mazabarsu, mazaba ta 6 dake unguwar Okeyinmi cikin garin Ado Ekiti, babban birnin jahar Ekiti a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.

Sanata Bode ya taba wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2009 zuwa 2011, ayin da dan uwansa Segun ya kasance dan majalisa a majalisar dokokin jahar Ekiti tun daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2007.

A jawabinsa, Sanata Bode ya bayyana dalilin shigarsa jam’iyyar APC, inda yace hakan baya rasa nasaba da kyawawan ayyukan cigaba da gwamnatin APC a jahar a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Kayode Fayemi take yi a jahar.

Da yake nasa jawabin, mataimakin gwamnan jahar, Egebeyemi ya bayyana jin dadinsa da dawowar jigogin biyu cikin jam’iyyar APC, inda ya basu tabbacin gwamnatin jahar Ekiti za ta cigaba da yin ayyukan da zasu inganta rayuwar talaka, saboda talakawa ne a gabanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel