Mai dokar bacci: Ana bincikar wani babban jami'in 'yan sanda a Najeriya

Mai dokar bacci: Ana bincikar wani babban jami'in 'yan sanda a Najeriya

Sashin dake kula da manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Yaba, jihar Legas ya fara gudanar da bincike bisa zargin cin hanci da ake yiwa DPO mai kula da sashin Pen Cinema mai suma Harrison Nwabuisi.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa, DPO tare da wandasu jami’an ‘yan sanda ana zargin sune da amsar na goro daga wajen mazauna unguwar Alimi Ogunyemi dake Ijeiye.

Mai dokar bacci: Ana bincikar wani babban jami'in 'yan sanda a Najeriya
Mai dokar bacci: Ana bincikar wani babban jami'in 'yan sanda a Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya shirya saida dam 6 na Najeriya

Shi dai Nwabuisi ya karyata amsar kudin belin, ba kamar yadda mazauna unguwar suka nace a kan suna biyan kudin ga shi DPO.

Wakilinmu ya labarta mana cewa a ranar Laraba ne shi Nwabuisi ya jagoranci ‘yan sanda suka je wannan unguwa suka kama mutane ba tare da laifin komi ba. Sun dai kama mutane guda 37 tare da neman sai an ba su kudin beli a kan naira 15,000 ga kowannan su.

Wani jami’a mai suna Bigi ana zargin ya amsa naira 30,000 ga mutane guda uku da aka kama. Kwamishinar Jihar Legas Edgal Imohimi ya dakatar da DPO, sannan ya nada jami’an da zai gudanar da binciken lamarin.

Mataimakin kwamishinan na Yaba DCP Yetunde Longe shi ne zai jogoranci binciken. Wani wanda al’amarin ya faru a gaban idanonsa mai suna Ibrahim Aranjure ya ce, DCP ya tutube shi a ranar Litinin, ya kuma kara da cewa ya ziyarci ofishin ‘yan sanda tare da mutane uku.

Ibrahim shi dai dan’uwan ne ga Sheriff wanda aka kama tare da mutane uku, inda aka bukaci sai sun biya naira 30,000 kudin beli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel