Rigimar magoya bayan APC: Mutum biyu sun mutu, an kone motoci 35

Rigimar magoya bayan APC: Mutum biyu sun mutu, an kone motoci 35

Alamu na nuni da cewar zaben gwamna da ‘yan majalisar dokoki a jihar Legas kan iya haifar da rikici idan aka yi la’akari da yadda tsagin magoya bayan jam’iyyar APC su ka yi wani kazamin rikici a da yammacin yau, Alhamis.

A kalla mutane biyu su ka rasa ran su yayin da aka kone motoci 35 da lalata shaguna a rikicin da ya barke tsakanin tsagi biyu na jam’iyyar APC a Oto-Awori da ke Ijanikin a garin Legas.

Rikicin ya kaure ne tsakanin magoya bayan dan takarar kujerar majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar karamar hukumar Ojo a zaben da za a yi ranar Asabar mai zuwa da kuma abokin takarar sa da su ka buga a zaben cikin gida kuma yak e ikirarin an yi ma sa kwacen nasarar da ya samu.

Rigimar magoya bayan APC: Mutum biyu sun mutu, an kone motoci 35
Rigimar magoya bayan APC a Legas
Asali: Twitter

Rikicin ya afku ne a lokacin da dan takarar da ake kira Jafo ya kai ziyarar ban girma fadar Oloto na Awori.

DUBA WANNAN: Jihohi 7 da ba za a yi zaben gwamna ba ranar Asabar

Rahotanni sun bayyana cewar an fara samun hargitsi ne a lokacin da magoya bayan Bibire, dan takarar da bai samu tikitin jam’iyyar APC ba, su ka yi kokarin hana Jafo shiga fadar basaraken bisa dalilin cewar shine ya sanadiyyar hana dan takarar su damar sa ta yin takara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel