Buhari ya yi mi'ara koma baya a kan furucin tsananin da za a fuskanta a zangon sa na biyu

Buhari ya yi mi'ara koma baya a kan furucin tsananin da za a fuskanta a zangon sa na biyu

Kasa da mako guda bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa na gaba zai yi zafi sosai, shugaban kasar ya sauya lafazin nasa a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, inda yace shekaru hudu da zai yi anan gaba zai zamo sanyayye kuma mai inganci.

Buhari wanda ya dauki alkawarin yayinda ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar kwadago a fadar shugaban kasa ya kara da cewa mulkinsa na gaba zai kasance mara rashawa.

Buhari ya yi mi'ara koma baya a kan furucin tsananin da za a fuskanta a zangon sa na biyu
Buhari
Asali: Depositphotos

Hakazalika Buhari yace gwamnatinsa na gaba za ta mayar da hankali ga cika alkawaran zaben da ya dauka na yaki da cin hanci da rashawa, habbaka tattalin arziki da kuma yakar rashin tsaro.

DUBA WANNAN: Dahiru Bauchi: Shugaban kungiyar Izala ya fasa kwai a kan wasikar kulla yarjejeniya da El-Rufa'i

Ya kuma ce zai zuba idanu domin samun bukatu daga shugabannin kwadago kan yadda za su hada hannu da zai taimaka wa gwamnatin tarayya wajen cimma manufofinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel