Magudin zabe: ‘Yan sanda sun kama mutane 10 a Katsina

Magudin zabe: ‘Yan sanda sun kama mutane 10 a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta sanar da cewar ta kama mutane 10 da su ka aikata laifuka daban-daban yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Katsina, Sanusi Buba, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a yau, Alhamis, yayin sanar da shirin da rundunar ‘yan sanda ta yi domin tunkarar zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki da za a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

A cewar sa, laifukan wadanda aka kama sun hada da kokarin hana gudanar da zabe da kuma saba ka’idojin zabe.

Rgowar laifukan sun hada da yin taro ba bisa ka’ida ba, damun jama’a, da amfani da mugggan makamai domin firgita ma su kada kuri’a a lokacin zabe.

Magudin zabe: ‘Yan sanda sun kama mutane 10 a Katsina
'Yan sanda sun kama mutane 10 a Katsina
Asali: Depositphotos

Kwamishinan ya kara da cewa tuni an gurfanar da mutanen a gaban kotu.

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda za ta kara tsaurara tsaro a kananan hukumomi 9 saboda kusancin su da jejin Rugu da ‘yan ta’adda ke buya.

DUBA WANNAN: Ban mutu ba, ina nan da rai da lafiya ta – Matashin da ya yi iyo a kwata saboda Buhari

A shirye mu ke don ganin an yi zabe lafiya a fadin jihar Katsina musamman wuraren da ke fama da kalubalen tsaro.

“Dokar takaita zirga-zirga ranar zabe har yanzu tana nan daram kamar yadda aka saba daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma kuma duk wanda mu ka samu da laifin karya ta za mu kama shi sannan mu gurfanar da shi,” a cewar Buba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel