Cikin Bidiyo: Atiku ya kirayi magoya bayan sa kan zaben PDP yayin zaben gwamnoni na ranar Asabar

Cikin Bidiyo: Atiku ya kirayi magoya bayan sa kan zaben PDP yayin zaben gwamnoni na ranar Asabar

- Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yiwa al'ummar Najeriya jawabai yayin gabatowar zaben gwamnoni da za a gudanar a ranar Asabar

- Tsohon Mataimakin shugban kasar cikin wani sabon faifan bidiyo ya kirayi magoya bayan sa da su dangwalawa jam'iyyar PDP kuri'un su a kowane mataki yayin zaben ranar 9 ga watan Maris

- Atiku ya mika godiyar sa da jinjina dangane da soyayyar da ya samu yayin zaben shugaban kasa da aka gudanar makonni biyu da suka gabata

Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya yi kira ga magoya baya da su fito kwansu da kwarkwata tare da tururuwa wajen dangwalawa jam'iyyar PDP kuri'u yayin zaben gwamnoni na ranar 9 ga watan Maris.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku ya yi wannan kira a yau Alhamis, 7 ga watan Maris na shekarar 2019 cikin wani sabon faifan bidiyo da ya shimfida a shafin sa na zauren sada zumunta da ake kira Twitter.

Cikin Bidiyo: Atiku ya kirayi magoya bayan sa kan zaben PDP yayin zaben gwamnoni na ranar Asabar
Cikin Bidiyo: Atiku ya kirayi magoya bayan sa kan zaben PDP yayin zaben gwamnoni na ranar Asabar
Asali: UGC

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga magoya bayan sa da su dangwalawa jam'iyyar PDP kuri'un su a kowane mataki yayin zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki na jiha da za a gudanar a jibi Asabar.

Wazirin Adamawa ya kuma mika godiyar sa da kuma mafi kololuwar jinjina sakamakon tsagwaran soyayyar da ya samu yayin babban zabe na shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun da ya gabata.

KARANTA KUMA: Sakamakon Zabe: Buhari ya gurɓata Kotun Koli, ba bu lallai Atiku ya cimma nasara - Agbakoba

Baya ga umarni da kyakkyawa da kuma hani da munanan ababe yayin zabe, Atiku ya ce muddin mai nema ya na tare da samu ba bu wanda ya isa ya dakilewa jam'iyyar PDP nasara domin kuwa "Zakaran da Mai Duka ya nufa da cara, ko ana Muzuru ana Shaho sai ya yi".

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, yayin ci gaba da kalubalantar sakamakon babban zabe, a jiya Laraba kotun sauraron korafe-korafen zabe ta umarci hukumar INEC kan mikawa Atiku kayayyakin da ta ribata yayin zabe domin gudanar da binciken sa.

Kalli Faifan Bidiyo na jawaban Atiku

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel