Gwamnatin Sokoto ta tura dalibai 50 kasar Ukraine domin karatun Likitanci

Gwamnatin Sokoto ta tura dalibai 50 kasar Ukraine domin karatun Likitanci

Gwamnatin jihar Sokoto ta kammala duk wani shirye-shire domin daukar nauyin akalla dalibai 50 yan asalin jihar zuwa kasar Ukraine domin karantar kimiyar likitanci.

Yayinda yake jawabi ga daliban, Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Bashar ya shawarci daliban da su kasance abun koyi na kirki ga jihar.

Ya bayyana cewa gwwamnatinsa na cika alkawaran da ta dauka da horar da dalibai 200 a jihar kan kimiyar likitanci a kasar waje domin yi kari akan daliban gwamnatocin baya da ke waje.

Gwamnatin Sokoto ta tura dalibai 50 kasar Ukraine domin karatun Likitanci
Gwamnatin Sokoto ta tura dalibai 50 kasar Ukraine domin karatun Likitanci
Asali: Depositphotos

Gwamnan ya bayyana cewa a yanzu haka dalibai 100 ne a kasar Indiya, 20 a kasar Ghana da kuma wasu 30 a Sudan inda suke karantar fanni daban-daban na kimiyar likitanci.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP ta rasa wasu manyan mambobinta inda suka koma APC

Ya bayyana cewa sauran 50 da suka rage za su tashi zuwa kasar Ukraine bayan zabe mai zuwa yayinda yayi alkawarin ci gaba da tura Karin dalibai idan har yayi nasarar zarcewa a matsayin gwamna.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa akalla shugabannin kungiyar Fulani 66 tare da yan arewa 1000 daga kananan hukumomin Silame, Wamakko, Tangaza, Gudu, Yabo, Shagari, Binji da Tureta duk a jihar Sokoto, sun bayyana komawar su jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, 6 ga watan Maris.

Shugaban jam’iyyar APC na kungiyar Fulani a fadin kasa, Alhaji Shehu Aliyu ya bayyana cewa masu sauya shekar sun bar tsohuwar jam’iyyar su ne saboda sakacin shuwagabannin PDP, sannan ya kara da cewa a halin yanzu alúmman Fulani na fuskantar barazanar rashin isasshen wuraren kiwon dabbobi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel